
Matthew Achigbe, shugaban jam’iyar APC na jihar Cross River ya mutu.
Shugaban jam’iyar ya mutu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi akan titin Afikpo dake jihar Ebonyi ranar Asabar.
Achigbe na kan hanyarsa ta komawa gida daga jihar Enugu inda ya halarci wani taron coci.
Sauran mutane biyu dake cikin motar suma sun rasa rayukansu a hatsarin.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin,John Ochala mataimakin shugaban jam’iyar na jihar ya ce dukkansu suna cikin kaduwa tun lokacin da suka samu labarin faruwar lamarin.
“Ya halarci taron cocin katolika kuma yana kan hanyarsa ta komawa Obubra lokacin da lamarin ya faru,”ya ce.