Shugaban ƴan ta’adda ya mika wuya a Katsina, bayan ya sako mutane 10

Wani babban shugaba a cikin ’yan ta’adda ya mika wuya ga dakarun sojojin Najeriya a karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina, inda ya sako mutane 10 da ya yi garkuwa da su, ciki har da mata bakwai da yara uku.

Baya ga hakan, jagoran ’yan ta’addan ya kuma mika manyan bindigogi guda biyu kirar AK-47 ga sojojin, wanda hakan ke nuna aniyarsa ta barin ta’addanci da rungumar zaman lafiya.

Wannan ci gaban ya fito ne daga rahoton masanin tsaro, Zagazola Makama, wanda ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wannan mika wuya babbar nasara ce a kokarin karya lagon ’yan ta’adda a jihar.

A wani samame dabam, dakarun rundunar Operation FANSAN YANMA sun dakile wani hari na ƴan bindiga.

More from this stream

Recomended