Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2025

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2025 bayan amincewar Majalisar Dokoki ta Kasa.

Majalisar ta amince da kasafin Naira tiriliyan 54.99, wanda a baya ya kasance Naira tiriliyan 49.7.

Sai dai daga bisani, bayan bukatar karin da Shugaba Tinubu ya nema, an daga kasafin zuwa Naira tiriliyan 54.2.

Binciken kasafin ya nuna cewa an ware Naira tiriliyan 3.645 domin kasafin dokoki (Statutory Transfers), Naira tiriliyan 14.317 domin biyan basussuka, Naira tiriliyan 13.64 domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati, da kuma Naira tiriliyan 23.963 domin manyan ayyukan raya kasa.

More from this stream

Recomended