Shugaba Tinubu Ya Dawo Gida Daga Ziyarar Aiki a Ƙasar Faransa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo gida daga ziyarar aikin da ya kai a ƙasar Faransa.

Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 9 na dare, inda manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi a sashin shugabannin ƙasa.

Tun kafin dawowar shugaban, mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya sanar a shafinsa na X cewa, “Shugaba Bola Tinubu zai dawo gida yau.”

A baya fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban zai dawo bayan bukukuwan Ista, sakamakon ƙararrawar da ‘yan Najeriya suka fara daga game da jinkirin dawowarsa a daidai lokacin da hare-haren ‘yan bindiga ke kara ta’azzara a jihohin Filato da Benue.

Onanuga ya bayyana cewa shugaban na bin dukkan abubuwan da ke faruwa a gida, tare da ci gaba da mu’amala da jami’an gwamnati da ya nada.

Tinubu ya tafi Faransa ne a ranar 2 ga Afrilu, 2025 domin wata gajeriyar ziyara ta aiki.

A lokacin zamansa na makonni biyu a birnin Paris, Tinubu ya gana da babban mai ba da shawara kan harkokin Afirka na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Massad Boulos.

A yayin ganawar, Boulos ya bayyana sha’awar gwamnatin Amurka wajen karfafa dangantakar kasuwanci da Najeriya, abin da Tinubu ya yaba da shi musamman ganin yadda manufofin haraji na shugaba Trump suka shafi kasuwancin ƙasashen waje.

Sauran batutuwan da aka tattauna sun haɗa da yunƙurin kafa zaman lafiya mai ɗorewa a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC), tare da hadin gwiwar ƙasashen yankin da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

Daga nan shugaban ya zarce London inda ya ci gaba da ganawa da muhimman jami’an gwamnati da kuma tattaunawa kan muhimman lamurra da ke shafar kasa.

More from this stream

Recomended