Shin Buhari na jin tsoron Kwankwaso ne?

[ad_1]

Kwankwaso

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka faru a fagen siyasar Najeriya wannan makon, wanda da alama ya share fage kan al’amuran da za su faru nan gaba, shi ne hana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso amfani da babban filin taron nan na Eagle Square da ke tsakiyar Abuja, babban birnin kasar wajen kaddamar da bukatarsa ta yin takarar shugaban Najeriya a 2019 karkashin jam’iyyar PDP mai hamayya.

Dan majalisar ta dattawa da ke wakiltar Kano ta Tsakiya shi ne ya zo na biyu a zaben fitar da gwanin takarar shugabancin kasa da jam’iyyar APC ta gudanar a 2014.

A wasikar da kamfanin da ke kula da filin taron, Rasy International and Properties Ltd., ya aike wa ofishin Sanata Kwankwaso ranar 20 ga watan Agusta ya amince Sanatan ya kaddamar da gangaminsa ranar 29 ga watan inda ya bukaci ya biya sama da N2m kudin amfani da filin.

Da alama hakan ne ya bai wa Sanata Kwankwaso da magoya bayansa kwarin gwiwar ci gaba da shirye-shiryen tafiya Abuja domin yin abin da suka kira gagarumin taro.

Sai dai kwana biyu kafin taron, wato ranar 27 ga watan Agusta, kamfanin ya sake aike wa da Sanatan wata wasikar – a wannan karon ya ce ya soke amincewar da aka yi ta ba da wurin taron.

‘Ba a taron siyasa ranar aiki’

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Kwankwaso For President 2019

Image caption

Dubban magoya bayan Sanata Kwankwaso ne suka amsa kiran sa na kaddamar da takara

Kamfanin na Rasy ya ce ya dauki matakin ne saboda “taron da za a yi na siyasa ne kuma ranar 29 ga watan Agusta ranar aiki ce don haka yin taron zai kawo cikas ga mutanen da ke zuwa babbar sakatariyar gwamnatin tarayya aiki.”

Sai dai wasu masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin kamfanin da ya dauki matakin hana Sanata Rabi’u Kwankwaso yin taro a filin na Eagle Square ba su yi nazari domin bayar da gamsasshen dalilin hana amfani da filin ba.

Ba wannan ne karon farko da ‘yan siyasa ke amfani da filin wajen gudanar da harkokinsu ba a ranakun aiki, ciki kuwa har da Janar Muhammadu Buhari, wanda a 2014 ya kaddamar da takararsa ta shugabancin kasar a filin kuma ranar aiki.

Don haka mutane da dama basu gamsu da wannan dalilin da kamfanin Rasy ya bayar.

Shi ma Sanata Kwankwaso ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta hana shi yin amfani da filin ne domin cimma wani buri na siyasa.

Sai dai ya kara da cewa hakan ba zai girgiza shi ba, don haka ne ya nemi wani fili a unguwar Jabi da ke Abuja inda ya kaddamar da takararsa.

Manya da kananan ‘yan siyasa – ciki har da magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki – sun soki matakin hana Sanata Kwankwaso amfani da Eagle Square.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da shi ma ke da sha’awar takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, ya yi tur da matakin inda ya ce “ranar 15 ga watan Oktoba na 2014, gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar PDP ta bar Janar Muhammadu Buhari ya yi amfani da filin domin kaddamar da takararsa ta shugabancin kasar ba tare da wata musgunawa ba.”

Shi ma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda ya ayyana aniyarsa ta yi wa PDP takara ya ce hana Sanata Rabi’u Kwankwaso takkadamar da takararsa a Eagle Square wata mummunar alama ce ga mulkin dimokradiyya da bai wa kowanne dan kasa damar zabin abin da yake so.

Me ya sa aka hana Kwankwaso sakat?

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Presidency

Image caption

Sanata Kwankwaso ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi musu adalci ba

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce kamfanin da ke kula da filin ne yake da wuka da nama kan batun amfani da shi.

Ba wannan ne karon farko da ake hana tsohon gwamnan jihar Kanon yin abin da yake so ba.

A watan Janairun wannan shekarar, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bukaci Sanata Kwankwaso ya janye aniyarsa ta kai ziyara jihar, tana mai cewa ziyarar tasa ka iya haifar da yamutsi.

A wancan lokacin, ana shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar- wacce ya taba yi gwamna- inda ake ganin ziyarar tasa ka iya yin kafar-ungulu ga burin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba ya jituwa da Sanatan, na tabbatar da nasarar jam’iyyar APC.

Sai dai bayan da aka kai ruwa-rana, Sanata Kwankwaso ya janye aniyarsa ta kai ziyarar inda ya ce ba ya so ya yi sanadin zub da jinin ko wanne mutum ko da yake mukarraban gwamnatin jihar sun ce tsoro ne ya hana shi zuwa Kano.

Masu sharhi kan siyasa dai na ganin hana tsohon gwamnan jihar Kanon sakat wata dabara ce ta dakushe kaifin goyon bayan da yake da shi musamman a Kano, inda can ne Shugaba Buhari ke ikirarin zama tushen siyasarsa.

“Zai iya yiwuwa hana shi taron Abuja da zuwa Kano arashi ne amma hakan zai sa a rika zargin cewa ana yi masa makarkashiya ne kawai. Kuma shi dan siyasa ne da ke da farin jini da magoya baya, don haka zai iya yi wa Shugaba Buhari barazanar sake cin zabe,” in ji Kabiru Sa’idu Sufi, Malamin da ke koyar da harkokin siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta jihar Kano.

Kamar yadda masanin harkokin siyasar ya fada, wasu na ganin shugaban kasar zai fuskanci babban kalubale a jihar kasancewa tsofaffin gwamnonin jihar biyu – Malam Ibrahim Shekarau da Sanata Kwankwaso – suna jam’iyyar PDP mai hamayya.

Kazalika wasu na da ra’ayin cewa shugaban kasar bai yi wa jihar, wacce ta fi kada masa kuri’a tun da ya ayyana bukatarsa ta shiga siyasa, abin kirki ba tun da aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2015.

Sai dai magoya bayan Shugaba Buhari sun sha cewa shugaban na “kowa” ne don haka bai kamata a rika yi masa kallon na wata jiha ba, suna masu cewa idan ya sake lashe zabe a 2019 zai kawo gagarumin ci gaba a jihar da ma kasar baki daya.

Ga karin wasu labarai da za ku so ku karanta:

[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...