Shettima Ya Ziyarci Aisha Buhari Da ’Ya’yan Marigayin Shugaban Kasar a London

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya kai ziyarar ta’aziyya ga uwargidar tsohon Shugaban Kasa marigayi Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, a birnin London na kasar Birtaniya.

Shettima, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya da ke London domin dauko gawar Buhari zuwa gida, ya kuma gana da ’ya’yan marigayin.

Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna Shettima tare da Hajiya Aisha da kuma wasu daga cikin ’ya’yan marigayin a cikin yanayi na alhini da jimami.

An ruwaito cewa Buhari ya rasu ne a asibiti da ke London yayin da yake karbar magani kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Buhari ya rike madafun iko a matsayin Shugaban Kasa na mulkin soja, sannan daga bisani ya zama zababben shugaban kasar Najeriya a mulki na dimokuradiyya.

A lokacin mulkinsa, Buhari ya shafe akalla kwanaki 225 yana jinya a kasashen waje, inda mafi dadewa daga ciki ya kasance a watan Mayu na 2017, lokacin da ya shafe kwana 104 a London.

Ana sa ran Shettima da sauran mambobin tawagar gwamnatin tarayya za su dawo Najeriya da gawar marigayin shugaban kasa a ranar Talata.

An tsara gudanar da jana’izar Buhari a wannan ranar Talata, a mahaifarsa ta Daura da ke Jihar Katsina.

More from this stream

Recomended