Shehu Sani zai bayyana sabuwar jam’iyar da ya koma cikin kwanaki biyu

Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya ce fitarsa daga jam’iyar APC ba alama ce dake nuna cewa ya daina siyasa ba.

Sani ya fice daga jam’iyar ta APC biyo bayan tirka-tirkar da ta biyo bayan zaben fidda gwani na jam’iyar APC.

Shugabancin jam’iyar na kasa ya yiwa sanata Shehu Sani alkawarin tikitin takara ba tare da hamayya ba amma kuma daga bisani jam’iyar ta mikawa hukumar zabe ta kasa sunan,Uba Sani mai taimakawa gwamna Nasiru El-rufa’i El-rufa’i kan harkokin siyasa a matsayin wanda zai yi mata takara a mazabar Kaduna ta tsakiya.

Hakan ya jawo ficewarsa daga jam’iyar ta APC.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter dan majalisar dattawan ya ci alwashin tsayawa zabe a shekarar 2019 inda ya yi alkawarin bayyana sabuwar jam’iyyar sa cikin kwanaki biyu

.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...