Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta kori tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga cikinta tare da hana shi hulɗa da kowanne bangare na jam’iyyar na tsawon shekaru 30.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar, SDP ta bayyana cewa matakin ya yi daidai da kundin tsarin mulkinta da dokokin Najeriya.
A cewarsa: “El-Rufai an kore shi daga jam’iyyar tare da haramta masa neman komawa ko nuna alaka da kowacce alama, siffa ko ayyuka da suka shafi SDP na tsawon shekaru 30 daga yau.”
Jam’iyyar ta kuma gargadi mambobinta da su guji yin hulɗa da El-Rufai ko wasu da ba sa wakiltar muradunta.
Idan ba a manta ba, El-Rufai ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa SDP, kafin daga bisani ya shiga wata kawancen jam’iyyu da suka amince da ADC a matsayin dandalinsu na siyasa kafin zaben 2027.
SDP Ta Kori El-Rufai, Ta Haramta Masa Komawa Jam’iyyar Na Tsawon Shekara 30
