Saudiyya Ta Ga Jinjirin Watan Shawwal

Hukumomin Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a yau Asabar, wanda ke nuna ƙarshen watan Ramadan da kuma fara bukukuwan Sallah.

Shafin Inside the Haramain ya ruwaito cewa kwamitin duba wata na Saudiyya ya cimma matsaya bayan shafe lokaci suna bincike.

Saboda haka, gobe Lahadi, 30 ga Maris 2025, zai kasance 1 ga watan Shawwal 1446, wanda ke nufin ranar Ƙaramar Sallah a Saudiyya.

A halin yanzu, ana jiran sakamakon kwamitocin duba wata a Najeriya da wasu ƙasashe domin tabbatar da ranar Sallah a yankunansu.

More from this stream

Recomended