Saraki,Dogara: Dalilin da yasa ba za mu kira zaman majalisa ba

[ad_1]








Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun ce babu wata rana da aka saka da majalisun biyu za su zauna.

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya shawarci majalisun biyu kan su katse wutun da suke domin su duba kasafin kudin da ya tura musu na naira biliyan ₦242 domin gudanar da zaɓen shekarar 2019.

A makon da ya wuce Yusuf Lasun mataimakin shugaban majalisar wakilai ya bayyana cewa majalisar za ta zauna ranar Talata domin tattauna batun kasafin kudin.

Amma yan majalisar basu samu sanarwar sake zaman ba har ya zuwa ranar Litinin.

A wata sanarwa ranar Talata mai dauke da sahannun Yusuf Olaniyonu da kuma Turaki Hassan masu taimakawa Saraki da Dogara kan harkokin yada labarai sun bayyana cewa babu wani rahoto da za ayi muhara akansa saboda kwamitin da aka dorawa alhakin duba bukatar da shugaban kasar ya aikewa majalisar bai taba zama ba tukunna.

Shugabannin majalisun biyu sun bayyana cewa ba dai-dai bane su kira zaman majalisun alhalin babu rahoton da za a tattauna akai




[ad_2]

More News

Atiku ya bayar da tallafin miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 100 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

An saki Sowore bayan kama shi da aka yi  a filin jirgin saman Lagos

Omoyele Sowore ɗantakarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyar AAC a zaɓen 2023 a ranar Litinin ya ce an tsare shi na gajeren lokaci a...

Mutanen Sokoto na ta murnar kashe ƙasurgumin ɗanbindigar nan Halilu Buzu

Mazauna yankin Sokoto da kewaye na murnar kashe wani kasurgumin shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Halilu Buzu, da sojojin Najeriya suka yi a farmakin da...