Sanata Natasha Ta Zargi Akpabio Da Yahaya Bello Da Yunkurin Kashe Ta

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi zargin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, sun shirya makircin hallaka ta.

Sanatar ta bayyana wannan zargi ne yayin da take jawabi ga magoya bayanta a lokacin dawowarta gida, inda suka tarbe ta da murna a ranar Talata.

A cewarta, kodayake ba a bayyana shirin ba a fili, amma an sanar da Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

A halin yanzu, ana ci gaba da bibiyar lamarin yayin da jama’a da magoya bayan Natasha ke nuna damuwa kan tsaron rayuwarta.

More from this stream

Recomended