Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Munya na Jihar Neja, Aminu Najumei, ya bayyana cewa sakataren majalisar, Daina Usman, wanda aka sace a daren Alhamis, ya samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa da shi ranar Juma’a.
Shugaban majalisar, wanda ya bayyana wannan a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan labarin sace sakataren majalisar, ya ce Usman ya tsere daga hannun masu garkuwa da shi lokacin da ‘yan fashi ke neman wuri don ɓoye su.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashi sun sace Usman tare da matarsa, yara biyu, da wani mutum a harin da aka kai da dare a Sarkin Pawa, Jihar Neja.
An ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare lokacin da ‘yan fashin suka shiga gidan Usman da ke kusa da bakin ruwa a Sarkin Pawa.
Sai dai an gano cewa sakataren majalisar ya tsere lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin ɗauke su zuwa wani wurin ɓuya, inda ya bar matarsa da yaransa.
An kuma gano cewa bayan sace sakataren da wasu, ‘yan fashin sun tsere da su zuwa karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Sakataren Majalisar Karamar Hukumar Munya Ya Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa da Shi
