Sabon Fagen Zaman Lafiya da Ci Gaban Birnin Gwari: BEPU Ta Yabi Tinubu da Gwamnan Kaduna

Kungiyar cigaban Masarautar Birnin Gwari (Birnin Gwari Emirate Progressives Union — BEPU) ta bayyana farin cikinta kan dawowar zaman lafiya da kuma sabbin shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a yankin.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dr. Isah Muhammad, ya fitar a ranar 21 ga Yuni, 2025, BEPU ta bayyana cewa rikice-rikicen da suka dabaibaye yankin Birnin Gwari na tsawon shekaru — wadanda suka janyo kashe-kashe, sace-sacen mutane, kona gonaki da rushe kauyuka — sun ragu da fiye da kaso 95 cikin 100.

Sanarwar ta ce: “Tun daga watan Nuwamba 2024 zuwa yau, babu rahoton kisan kai ko satar mutane a Birnin Gwari. Wannan shekarar ta 2025 ita ce mafi alheri da dimbin manoma suka koma gona ba tare da tsoro ba.”

BEPU ta ce hanyoyin da suka jima a cikin hadari yanzu sun koma amintattu, inda manyan motoci da kananan motocin haya ke zirga-zirga ba tare da fargabar harin ’yan bindiga ba. Kasuwannin hatsi da na dabbobi sun sake farfadowa, har ma sun wuce yadda suka kasance a baya.

Kungiyar ta bayyana wannan ci gaba a matsayin sakamakon wata yarjejeniya ta zaman lafiya da aka cimma da kungiyoyin makamai, karkashin jagorancin Gwamnatin Jihar Kaduna tare da goyon bayan Gwamnatin Tarayya da shugabannin al’umma na Birnin Gwari.

A cewar BEPU, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe lokacin da ya ziyarci Birnin Gwari. A wata ziyararsa ta kwanan nan a jihar Kaduna a ranar 19 ga Yuni 2025, don kaddamar da wasu ayyuka na Gwamna Uba Sani, Tinubu ya sanar da amincewar Majalisar Zartarwar Tarayya da sake gina manyan hanyoyi guda uku:

Kaduna zuwa Birnin Gwari (km 126)

Birnin Gwari zuwa Funtua (km 178)

Birnin Gwari zuwa Tegina har zuwa Mokwa


BEPU ta ce wannan al’amari na nuna irin jajircewar gwamnatin Tinubu wajen ganin an kawo ci gaba da yaki da matsalolin rashin tsaro a Arewa.

Kungiyar ta kuma yaba da shirye-shiryen Gwamna Uba Sani na kafa kasuwar zamani ta dabbobi da abattoir a Birnin Gwari, da kuma kulawarsa kan aikin titin Birnin Gwari–Randagi. BEPU ta bukaci kamfanin da ke aikin titin da ya gina da inganci da gaskiya.

Kazalika, kungiyar ta yi kira da a kafa Jami’ar Tarayya ta Harkokin Ma’adinai da Albarkatun Daji a Birnin Gwari, la’akari da irin albarkatun kasa masu daraja da yankin ke da su, musamman nau’o’in zinariya da ba su da kama a duniya.

BEPU ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta mayar da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da Kwalejin Daji da Injiniyan Gandun Daji daga Kaduna zuwa Birnin Gwari, domin rage gibin ilimi a yankin da kuma karfafa zaman lafiya ta hanyar ilimi da arziki.

Kungiyar ta kuma jaddada bukatar ci gaba da amfani da hanyoyin zaman lafiya wajen shawo kan matsalolin tsaro a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Neja.

BEPU ta jajantawa al’ummar Jihar Benue bisa kisan mutane da aka yi a can, tare da bukatar daukar matakai masu karfi na dakile hakan. Ta kuma mika ta’aziyyarta ga mutanen Mokwa a Jihar Neja da ambaliya ta shafa, tana mai bukatar gwamnatin tarayya ta tallafa musu cikin gaggawa.

Ta kara da yin tir da ayyukan haramtattun da ake yi a cikin Dajin Kamuku, musamman sare itatuwa da hakar ma’adinai da farautar dabbobin daji. Ta bukaci daukar matakin doka kan duk wanda ke da hannu, ciki har da ma’aikatan ciki.

A karshe, BEPU ta bukaci Sanata Lawal Adamu Usman da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya da ya kara zage damtse wajen inganta ilimi a Birnin Gwari. Wannan ya hada da samar da cibiyar jarrabawar JAMB/UTME, da daukar nauyin kudirin kafa jami’a a yankin da sauran shirye-shirye na ci gaban kasa.

BEPU ta ce tana nan a shirye don ci gaba da hadin gwiwa da dukkan matakan gwamnati domin tabbatar da dorewar zaman lafiya, ci gaba da walwala ga al’ummar Birnin Gwari.

More from this stream

Recomended