Rundunar ‘Yan Sanda Ta Janye Gayyatar Da Ta Yi Wa Sarkin Kano Sanusi

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, dangane da wani rikici da ya auku yayin bukukuwan Sallah da suka gabata a jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana a ranar Lahadi cewa Babban Sufetan ‘Yan Sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin janye gayyatar, amma ya bukaci rundunar jihar Kano ta samu bahasi ta bakin sarkin kan lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa an gayyaci Sarkin ne domin ya bada bayanin sa game da rikicin da ya barke bayan kammala sallar Idi, wanda ya yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Usman Sagiru da kuma jikkatar wasu da dama.

An rawaito cewa duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu na sarautar Kano da gwamnatin jihar cewa ba za a gudanar da Hawan Durbur ba a ranar Sallah domin kaucewa tashin hankali, Alhaji Sanusi ya hau doki bayan sallar Idi tare da rakiyar masu gadi na sa.

More from this stream

Recomended