
Rundunar Sojan Ruwan Najeriya yanzu haka na can tana lalata haramtattun matatun mai dake wurare daban-daban na mashigar ruwan yankin Niger Delta.
Hakan na zuwa ne biyo bayan rahoton binciken sirri da jaridar The Cable ta gudanar kan yadda barayin mai ke cin karensu babu babbaka a yankin na Niger Delta mai dimbin arzikin mai.
A rahoton wasu daga cikin masu fasa bututun man sun shedawa jaridar cewa suna bawa sojoji cin hanci kafin su gudanar da mummunan sana’ar tasu da kewa tattalin arzikin kasa barazana.
“Muna aiki tare da sojojin ruwa, ƴansandan ruwa, jami’an Civil Defence, da kuma sojoji duk da cewa a baya lamarin yakan kasance tamkar yaki amma yanzu sun sanmu,”ya ce.
Amma Sam Bura kwamandan jirgin yakin sojan ruwan Najeriya da ake kira Pathfinder dake Fatakwal ya musalta zargin bayan da ya dauki wasu yan jaridu na wasu kafafen yada labarai ciki har da wakilin jaridar The Cable inda suka zagaya mashigar ruwa ta Bille a ranar Lahadi.
Ya yin da suke zagawa jami’an sojan ruwan sun lalata tare da rushe gine-gine da dama da kuma lalata kayayyaki da barayin man suke amfani da su.