Rundunar soja: Zamu ladabtar da sojojin da suka yi bore a filin jirgin saman Maiduguri

[ad_1]








Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa sojojin da suka yi zanga-zanga a filin jirgin saman Maiduguri dake jihar Borno za su fuskanci ladabtarwa dai-dai da dokar aikin soja.

Makonni biyu da suka wuce wasu sojoji sunyi bore a filin jirgin saman bayan da suka yi zargin cewa ana shirin tura su bakin daga a yakin da ake da Boko Haram.

Da yake magana ya yin wani taro a Borno, A.M Dikko kwamandan rundunar samar da tsaro ta Operation Lafiya Dole, ya ce boren soja laifi ne dake jawo hukunci.

“Bama hukunci a soja , muna ladabtarwa ne, ladabi shine kashin bayan aikin idan babu ladabi to babu rundunar soja,”ya ce.

“Idan soja ya yi kuskure to dole a gyara masa.”

Dikko ya tunatar da sojojin da suka yi boren kan rantsuwar da suka yi lokacin da ake daukarsu aiki inda ya karfafa cewa dukkaninsu sun shiga aikin ne a kashin kansu.




[ad_2]

More News

Ribadu ya koka kan yadda jami’an tsaro suke sayarwa da ƴan ta’adda bindigogi

Mai bawa shugaban shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya ce wasu daga jami'an ƴan sanda da kuma sojoji suna ɗaukar bindigogi daga...

Gwamnan Legas Sanwo-Olu ya kara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 85,000

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana shirin gwamnatinsa na fara biyan sabon mafi karancin albashi na N85,000 ga ma'aikatan jihar.Sanwo-Olu ya bayyana hakan...

Sama da mutane 100 aka tabbatar sun mutu a gobarar hatsarin tankar mai a Jigawa

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane 140 a hatsarin gobarar tankar mai da ta faru a garin Majia dake kan...

Sojoji sun kashe ɗan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojan Najeriya na Birged Ta 21 dake aiki da rundunar Operationa Haɗin Kai dake aikin samar da tsaro a yankin arewa maso...