Rikicin NNPP a Kano: ‘Yan Majalisa Sun Yi Watsi da Dakatarwar Da Aka Yi Musu

Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta guda hudu daga Majalisar Dokoki ta Kasa bisa zargin aikata abubuwan da suka ci karo da muradun jam’iyya.

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Alhaji Hashimu Dungurawa, ya bayyana sunayen ‘yan majalisar da abin ya shafa da suka hada da Sanata Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Rogo, da Kabiru Rurum.

Sai dai wadannan ‘yan majalisar sun yi fatali da dakatarwar, inda suka bayyana ta a matsayin wani yunkuri na yaudara da ba bisa ka’ida ba.

A cikin wata sanarwa da suka fitar tare, sun ce “Dungurawa kawai wani ɗan kore ne da Kwankwaso ke amfani da shi, kuma ba shi da wata madafa a harkokin jam’iyya.”

Sun kara da cewa hukuncin da aka yanke kan su ba shi da wani tasiri, musamman tun bayan hukuncin wata kotu a Abia a ranar 1 ga Nuwamba, 2024, da ta tabbatar da Dr. Boniface Aniebonam a matsayin shugaban jam’iyyar NNPP na gaskiya, tare da korar Kwankwaso da mabiyansa daga jam’iyyar.

‘Yan majalisar sun zargi Kwankwaso da yin mulkin kama-karya a NNPP, suna masu cewa “Ya mayar da jam’iyyar tamkar wata harkar kasuwancinsa, inda ba ya mutunta hadin kai da tsarin dimokuradiyya.”

Sun kuma yi zargin cewa rashin halartar Kwankwaso a bikin daurin auren ‘ya’yan Sanata Kawu Sumaila da bikin yaye daliban Jami’ar Al-Istiqama da ke Sumaila na nuni da yadda yake raba kan ‘yan jam’iyyar.

Amma a nasa bangaren, Shugaban NNPP na Kano, Dungurawa, ya ce an dakatar da wadannan ‘yan majalisa ne saboda yawaitar cudanya da ‘yan adawa, tare da yin ayyukan da ke saba wa muradun jam’iyyar.

Ya ce kwamitin bincike zai duba lamarin, kuma idan har wadanda abin ya shafa suka nemi gafara, akwai yiwuwar a dauke dakatarwar.

More from this stream

Recomended