Rikicin Kaduna: ƴansanda sun kama mutane 32

Ƴansanda a jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutum guda tare da kama mutane 32 dake da hannu a rikicin da yafaru yan kwanakin nan.

An ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da aka kama sun yi kokarin kona wuraren ibada a unguwanni Hayin Banki da Kawo ya yin da aka kashe mutum guda a Kasuwar Magani aka kuma kama wani dauke da makami.

A wani bangaren kuma gwamnatin jihar ta sassauta dokar hana fita da aka saka a Kachia mai magana da yawun gwamnan jihar Samuel Aruwan shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Aruwan ya ce mazauna Kachia za su iya fita tun daga safiya har ya zuwa karfe biyar na yamma.

Ya kara da cewa mutanen dake aiki na musamman ne kadai aka amince su fita a lokacin da dokar hana fitar take aiki inda ya ce duk wanda ya fita za a kama shi a hukunta.

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...