Kiraye-kirayen ya biyo bayan wata hatsaniya ne a wasu unguwannin cikin kwaryar Jos, wanda ya kai ga rasa rayuka da kona gidaje da ya zuwa yanzu ba a tantance ba.
A cewar kwamandan rundunar tsaro ta STF, Manjo Janar Augustine Agundu, lamarin ya kasance da takaici ganin irin zaman tattaunawar da su ka yi da matasan karamar hukumar Jos ta arewa, kwatsam sai wani rikicin ya sake barkewa.
Shima kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Undie Adie, wanda ya bayar da sanarwa ta kafafen yada labarai ya bukaci mutane su kasance a cikin gidajensu. Ya ci gaba da cewa “duk wanda aka kama a waje za a damke shi a kuma hukunta shi.”
Da yake yiwa Muryar Amurka karin haske kan lamarin, Kwamishinan yada labarai, Yakubu Datti, ya ce lamarin ya baiwa kowa mamaki ganin yadda aka zauna da shugabannin addinai da shugabannin matasa da na unguwanni, inda kowa ya mika kai cewa za a yi tafiya tare sai gashi wannan rikici ya sake barkewa.