Rikici ya barke a Zamfara kan zaben fid da gwani

Rikicin Bungudu

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na cewa an samu barkewar tarzoma a garin Bungudu sakamakon jinkirin isar malaman zabe da kayan aiki.

Abokin aikinmu da ke birnin Gusau Ibrahim Isa ya ce mutanen gari ne suka fara kona tayoyi saboda rashin fara gudanar da zaben fid da gwani a kan lokaci.

Ya ce jami’an zabe sun isa garin da takardun kada kuri’a da ake ganin ba su kai yawan mutanen da suka fita don yin zaben ba, wanda hakan ne ya sa ‘yan jam’iyyar ta APC suka fusata.

Lamarin ya kai sai da ‘yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu hayaniyar da dawo da doka da oda.

Al’amarin dai ya dan lafa daga baya, sai dai ba a fara zaben ba don jami’an jam’iyya sun ce suna jiran hukuncin da uwar jam’iyyar ta kasa za ta yanke dangane da yadda za a gudanar da zaben.

A sauran sassan jihar ma mutane da dama sun fita don gudanar da zaben.

Daga bayanan da Ibrahim Isa ya tattara, ya shaida mana cewa har zuwa yanzu ba a fara zaben ba a mafi yawan sassan jihar.

Dama dai a farkon makon nan gwamnan jihar ta Zamfara Abdul’aziz Yari ya yi barazanar cewa ba za a yi zaben fid da gwani ba na APC din a jiharsa har sai an bi ka’idar da suka sani.

An dai samu sabani ne tsakanin gwamnatin jihar da kwamitin zabe a kan ka’idojin zaben, ciki har da batun rajistar da za a yi amfani da ita wajen tantance masu zabe.

Gwamna Yari ya yi watsi da tsarin zaben da kwamitin uwar jam’iyyar suka ce za su yi amfani da shi wanda ya ce ya saba ka’ida.

Kwamitin da uwar Jam’iyyar APC ta tura domin gudanar da zaben a Zamfara ya bukaci duk wadanda ke da kati a jihar su fito su yi zabe.

Sai dai gwamnan ya shaidawa BBC cewa ka’idar zaben da suka sani ita ce sai ‘yan jam’iyya kuma wadanda sunayensu ke cikin kundin rijista ne za su yi zaben.

More News

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...

AMBALIYA: Bafarawa ya ba wa al’ummar Sokoto gudunmawar naira biliyan 1

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya bayar da gudummawar Naira biliyan daya ga al’ummar Sokoto, domin rage radadin wannan annoba.An bayyana hakan...

Ƴanbindiga sun kai hari coci-coci a Kaduna, sun kuma yi garkuwa da mutane

Mutane 3 ne ake fargabar sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu 30 bayan wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a...