Rikici: Buhari na ziyara a Kaduna

Buhari

Hakkin mallakar hoto
Twitter/@GovKaduna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara jihar Kaduna da ke arewacin kasar wacce ke fama da rikici.

Gwamnan jihar Nasir Elrufai ya tarbi Shugaba Buhari a filin jiragen sojin saman kasar da ke Kaduna ranar Talata da safe.

Shugaban na Najeriya ya gana da sarakuna da malaman addinai da kuma shugabanninn al’umar da rikicin jihar ya shafa.

Jihar ta Kaduna ta fada rikici ne tun tsakiyar watan Oktoba a garin Kasuwar Magani lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kada bisani rikicin ya watsu zuwa birnin Kaduna da kewayensa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

A karshen makon jiya ne aka sake sanya dokar hana zirga-zirgar a birnin na Kaduna da kewaye da kuma wasu yankunan karamar hukumar Kachia bayan kisan da aka yi waani basaraken da masu satar mutane suka sace.

  • An tura jiragen yaki da sojin kundumbala Kaduna
  • Rikicin Kaduna: Zan tashi garin Gonin Gora — Elrufai

Sai dai daga bisani an sassauta dokar a birnin na kaduna da kewaye.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce jami’an tsaro sun kama akalla mutum 93 wadanda ake zargi da hannu a rikicin.

Ita ma rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta tura sojin kundumbala da jiragen yaki jihar Kaduna.

Lamarin ya sake rincabewa bayan da aka zargi wasu matasa a garin Gonin Gora da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja da yunkurin tare hanya da zummar kashe matafiya ranar Juma’a.

Daga bisani Gwamna Elrufai ya halarci wurin domin ganin matafiya basu fuskanci wata matsala ba.

Ranar Asabar, gwamman ya ce zai tashi garin na Gonin Gora dungurungun idan matasan garin suka ci gaba da tare mutane suna kashe su.

Da yake jawabi a filin “Hannu a Yawa” na gidan rediyon tarayya na Kaduna, Gwamna Elrufai ya ce “ina ba mutanen Gonin Gora shawara cewa wannan abin da matasansu suke yi su daina idan ba haka ba wallahi tallahi zan tashi garin.”

“Ba za mu yarda su rika rufe hanya su hana mutane shiga ko fita daga gari suna kashe su ba. Za mu sa jami’an tsaro su rika duba wurin amma idan ba su daina ba, garin da kan shi bai fi karfin gwamnati ba.”

More from this stream

Recomended