Ribadu: Tinubu Bai Gaji Gwamnati A Yanayi Mai Kyau Ba, Musamman Fannin Tsaro

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta gaji gwamnati mai matuƙar rauni, musamman ta fannin tsaro.

Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar Benue, inda ya jajanta wa gwamnatin jihar da al’umma kan kisan sama da mutane 72 da wasu ‘yan ta’adda da ke fakewa da sunan makiyaya suka yi.

Ya ƙalubalanci al’ummar jihar da su ba gwamnatin Tinubu dama tare da daina siyasantar da kisan da ake ci gaba da yi a jihar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya.

A cewarsa: “Rundunoninmu na ƙoƙari, amma ba zai yiwu a tura soja ko ‘yan sanda kowace ƙauye ba. Ku bamu dama, ku daina siyasantar da al’amuran tsaro.”

Ribadu ya ƙara da cewa: “Mun gaji gwamnati mai rauni ƙwarai, amma abubuwa sun fara inganta. Mun rage yawan tashin hankalin da muka tarar, kuma za mu shawo kan wannan matsalar nan ma.”

Gwamnan jihar Benue, Fasto Hyacinth Alia, ya bayyana cewa jihar na cikin mawuyacin hali tun daga 2011, tare da rasa rayuka da dama.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin makonni biyu da suka gabata, hare-hare da kisan gilla sun ƙaru a jihohin Benue da Filato. A sabuwar arangama ranar Talata, ‘yan bindiga sun hallaka mutane 11 a Afia da ke ƙaramar hukumar Ukum.

More from this stream

Recomended