Rashin aikin yi ya karu da kusan mutane miliyan 3 a Najeriya

A shekarar da ta gabata mutane miliyan 17 ne inda suka kai 20 a yanzu

A shekarar da ta gabata mutane miliyan 17 ne inda suka kai 20 a yanzu

Hukumar kiddidiga a Najeriya ta wallafa wani rahoto da yake nuna cewa yawan marasa aiki a kasar ya karu da kusan kashi 23 cikin 100.

Hakan na nuna cewa ‘yan Najeriya marasa aikin yi sun tasa ma Miliyan 20.

Hukumar ta bayyana cewa a wannan shekarar yawan mutane marassa aikin yi ya karu daga mutane miliyan 17 a shekarar 2017.

Masanin tattalin arziki Auwal Muhammad ya ce akwai alaka tsakanin rashin aikin yi da hauhawar farashi.

Ya bayyana cewa kokarin magance daya kan haifar da aukuwar daya.

“Yanzu abun da ake kokari shi ne mutane su iya dogaro da kansu, ba wai su dogara da gwamnati ba.”

Sai dai ya ce sakamakon wannan kididdiga ya danganta ne da inda gwamnati ta fi mayar da hankalinta yanzu.


Rashin aikin yi ya karu da kusan mutane miliyan 3 a Najeriya

A watan Maris din wannan shekarar ne gwamnatin Najeriyar ta sanar da farfadowarta daga karayar tattalin arziki da ta fuskanta a baya.

Ko a wancan lokacin, hukumar kididdigar ce ta fitar da rahoto da ke nuna cewa an samu ci gaba a fannoni da dama na tattalin arzikin kasar.

More from this stream

Recomended