Qatar 2022: Kasashe 48 ne za su je gasar cin kofin duniya

Gianni Infantino addresses delegates from the Asian Football Confederation

Gianni Infantino ya fara shugabancin hukumar Fifa ne a watan Fabrairun shekarar 2016

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Gianni Infantino ya ce kasashe 48 ne za su halarci gasar cin kofin duniya wacce za a yi a kasar Qatar a shekarar 2022.

A baya an shirya fara amfani da tsarin kasashe 48 ne a shekarar 2026, inda kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico za su karbi bakuncin gasar.

Sai dai wannan sauyin zai tilasta wa Qatar ta hada gwiwa da wasu kasashe a yankin Gabas ta Tsakiya don karbar bakuncin gasar, a cewar shugaban hukumar.

“Idan abu ne da zai yi wu, to me ye zai hana mu?” in ji shi.

“Muna duba yiwuwar hakan, muna tattaunawa da abokanmu a Qatar da sauran kawayenmu da ke yankin kuma muna fatan hakan mai yiwuwa ne.”

Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana a babban taron hukumar kwallo kafa ta nahiyar Asiya a sabuwar hedkwatar hukumar a birnin Kuala Lumpur a kasar Malaysia.

“Ina so a kara bai wa kowace kasa damar fafatawa a gasar,” in ji shi.

More from this stream

Recomended