PDP Ta Karyata Jita-Jitar Ficewar Gwamna Dauda Lawal Daga Jam’iyyar Zuwa APC a Zamfara

Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta musanta rade-radin da ke yawo cewa Gwamna Dauda Lawal ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Shugaban PDP na jihar, Jamil Jibo Magayaki, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne.

“Ina matsayin shugaban jam’iyyar PDP a wannan jiha, kuma idan Gwamna Dauda Lawal yana da niyyar komawa jam’iyyar APC, dole sai na sani,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa: “A matsayina na shugaban PDP a Zamfara, ina tabbatar muku cewa Gwamna Dauda Lawal na nan daram a jam’iyyarmu mai albarka.

“Wadannan jita-jita wani yunkuri ne daga wadanda ke jin tsoron nasarar shirinmu na CETO.”

Magayaki ya kara da cewa PDP na nan tare da Gwamna Dauda Lawal, tare da mai da hankali wajen samar da ingantaccen shugabanci ga al’ummar Zamfara.

More from this stream

Recomended