Obasanjo, Jonathan sun halarci nada Atiku matsayin Wazirin Adamawa

An nada tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a matsayin Wazirin Adamawa.

Nada shi mukamin na Wazirin Adamawa na nufin Atiku Abubakar shine na biyu mafi girman sarauta a masauratar bayan Lamidon Adamawa, Muhammad Barkindo .

Da yake magana a wurin taron, Barkindo ya ce an girmama Atiku ne da sarautar Waziri saboda dunbin gudunmawar da ya bayar ga cigaban Najeriya musamman ma jihar Adamawa inda tasirin taimakonsa ya shafi fannoni da dama.

“Atiku ya kuma taimaka sosai wajen hada kan mutanen Adamawa da kuma bayar da managartar shawarwari ga masarautar.”ya ce.

Mai martaba Lamidon Adamawa ya kara da cewa sarautar Waziri bata gado bace za a iya bawa kowane mutum da ya dace.

Ana sa jawabin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yabawa Lamido kan daga darajar sarautar Atiku da ya yi daga Turaki ya zuwa Waziri.

Obasanjo ya tabbatarwa da masauratar cewa sabon Wazirin na Adamawa zai gudanar da aikinsa cikin , mutunci, gaskiya,da kuma rikon amana.

Nadin sarautar ya samu halartar tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan,mataimakinsa Namadi Sambo, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma gwamnonin jihohin Sokoto, Taraba,Gombe da Bayelsa.

More from this stream

Recomended