NNPP Za Ta Gudanar Da Taron Gaggawa Bayan Ficewar Jiga-Jigan Jam’iyyar A Kano

Shugaban jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) reshen Jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya bayyana cewa jam’iyyar na shirin kiran taron gaggawa, biyo bayan ficewar wasu jiga-jiganta a jihar.

A ranar Alhamis ne wasu fitattun shugabannin NNPP suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC. Ciki har da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, wanda ke wakiltar yankin Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa; Kabiru Alhassan Rurum, wanda ke wakiltar mazabar Rano/Bunkure/Kibiya a Majalisar Wakilai, kuma tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano; Sha’aban Sharada, tsohon dan majalisar wakilai daga Kano Municipal; da kuma Aliyu Gini daga mazabar Dala.

Da yake jawabi ranar Juma’a, Doguwa ya ce ficewar ba ta zo masa da mamaki ba. Ya dora laifin hakan a kan bangaren Kwankwasiyya, yana mai zarginsu da hana zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar.

Ya ce, “Lokacin da na karɓi shugabancin jam’iyyar, na yi ƙoƙarin haɗa kowa da kowa. Amma bangaren Kwankwasiyya sun ƙi amincewa da shugabancina, kuma hakan ya hana ci gaban jam’iyyar.”

Doguwa ya alakanta ficewar da abin da ya kira wariya da rashin adalci a jam’iyyar, yana zargin shugabannin Kwankwasiyya da haddasa hakan. A cewarsa, hakan ne ya jawo gajiyawar wasu daga cikin mambobin jam’iyyar, har ta kai su ga sauya sheƙa.

Ya kara da cewa, “Ni da wasu jiga-jigai za mu kira taron gaggawa nan ba da jimawa ba domin nazarin lamarin da kuma yanke matsaya mai karfi.”

Doguwa ya musanta zargin cewa bangarensa na aiki ne da jam’iyyar APC, yana mai cewa, “NNPP jam’iyya ce mai cikakken inganci da ’yanci. Ba mu cikin wata tattaunawa da kowace jam’iyya.”

Game da takaddama tsakanin bangarensa da na Kwankwaso, Doguwa ya ce nasu ne sahihin shugabancin jam’iyyar da hukumar INEC ta amince da shi.

More from this stream

Recomended