Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya rage farashin lita ɗaya na man fetur daga N950 zuwa N935 a gidajen mansa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Wani mazaunin unguwar Kubwa, Abdullahi Hashim, ya ce, “Na lura da cewa farashin man ya sauka zuwa N935 a safiyar Asabar. Wannan ci gaba ne mai kyau.”
Bukola Adewole, wata mazauniyar birnin, ta ce, “Na fara ganin sabon farashin a wurin Wuse Zone 4 tun ranar Jumma’a. Tashar NNPCL da ke kan hanyar Kubwa Expressway yanzu ke nuna sabon farashin.”
Saukar farashin ya biyo bayan sanarwar da Matatar Man Dangote ta fitar na rage farashin man da take sayarwa ga dillalai daga N865 zuwa N835 a matakin ex-depot.
Dangote Refinery mai iya tace gangar danyen mai 650,000 a rana, ta bayyana cewa abokan hulɗarta kamar MRS da AP za su sayar da lita ɗaya tsakanin N890 zuwa N920 bisa ga wurin da tashar take.
Sai dai kuma, har yanzu wasu tashoshin man kamar MRS da ke Abuja ba sa saida man tun daga ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025 – ranar da Dangote Refinery ta sanar da saukar farashin ex-depot.
NNPCL Ta Rage Farashin Man Fetur a Abuja
