NNPC Ta Sanar da Rufe Matatar Mai ta Fatakwal Don Aikin Gyara


Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC Ltd) ya bayyana cewa daga yau Asabar, 24 ga Mayu, 2025, za a rufe Matatar Mai ta Fatakwal don gudanar da aikin gyara na tsawon lokaci.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na kamfanin, Femi Soneye, ya fitar.

A cewar Soneye, rufewar na wani bangare ne na aikin kula da kayan aiki da kuma tantance yadda matatar ke aiki domin tabbatar da ingantaccen aiki a nan gaba.

Sanarwar ta ce: “Kamfanin NNPC Ltd na sanar da jama’a cewa za a rufe Matatar Mai ta Fatakwal don gudanar da aikin gyara da nazari na dorewar aiki daga ranar 24 ga Mayu, 2025.”

“Muna aiki tare da dukkan hukumomin da suka dace, ciki har da Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Tsakiya da Ta Ƙasa (NMDPRA), domin tabbatar da cewa aikin zai gudana cikin nasara da gaskiya.”

Kamfanin ya kara da cewa zai ci gaba da bayar da bayani a kai a kai ta hanyoyin sadarwa na hukuma, tare da tabbatar da cewa yana ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantaccen tsaro a fannin makamashi a Najeriya.

More from this stream

Recomended