NLC Da TUC Sun Nuna Rashin Dacewar Ayyana Dokar Ta-Baci a Jihar Rivers

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da Kungiyar Hadin Gwiwar Ma’aikata (TUC) sun yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye abin da suka kira take hakkin dimokuradiyya, bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers.

A cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, shugabannin kungiyoyin biyu, Joe Ajaero na NLC da Festus Osifo na TUC, sun bayyana matsayinsu kan matakin da shugaban kasa ya dauka a ranar Talata.

NLC da TUC sun soki ayyana dokar ta-baci, inda suka ce hakan ba bisa doka ba ne kuma ya saba wa tsarin dimokuradiyya.

A cewar kungiyoyin, sauke gwamna, mataimakinsa da ‘yan majalisar dokokin jihar ba bisa ka’ida ba ne kuma hakan cin zarafi ne ga tsarin mulkin kasa.

An ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers ne a yayin jawabin da ya yi ga yan kasa a ranar Talata.

Daga bisani, ya rantsar da tsohon mataimakin hafsan sojin ruwa, Ibokette Ibas, a matsayin sabon mai kula da jihar.

A halin yanzu, har yanzu Majalisar Dokoki ta Kasa ba ta fitar da wata sanarwa ba kan batun, yayin da matakin ya jawo cece-kuce daga ‘yan siyasa da sauran al’ummomin kasa.

Shugabannin jam’iyyun adawa, ciki har da ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun PDP da Labour Party a zaben 2023, sun yi Allah wadai da matakin da Shugaba Tinubu ya dauka.

More from this stream

Recomended