Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana cewa yana iya ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaza gyara halin da Najeriya ke ciki.
Ndume ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise TV a ranar Talata, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnati ke tafiyar da harkokin kasa.
A ‘yan watannin nan, Ndume ya sha suka kan salon mulkin Tinubu, yana bukatar ganin an samu ingantaccen shugabanci daga wannan gwamnati.
“Idan na yanke shawarar barin APC, ba zan boye ba,” in ji Ndume. Ya kara da cewa: “Har yanzu ina da yakinin cewa Shugaba Tinubu zai iya gyara abubuwa. Amma idan ya kasa, hakan na iya sa na bar APC.”
Sanatan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake karbar sababbin mutane cikin APC, yana mai gargadin cewa hakan na iya haifar da illa ga jam’iyyar.
“Ina jan kunnen Tinubu cewa idan ya cigaba da haka, ko da kuwa yana karbar gwamnonin jihohi da sauran mutane cikin APC, hakan zai iya zama barazana ga jam’iyyar,” in ji Ndume.
Ya ci gaba da cewa: “Idan aka cika jirgi da yawa, hakan na iya haifar da kifewar jam’iyyar.”
Bayani daga Ndume na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun sauyin ra’ayi daga wasu ‘yan siyasa kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Tinubu, musamman ta fuskar tattalin arziki da tsaro.
Ndume Ya Ce Idan Tinubu Bai Gyara Harkokin Najeriya Ba Zai Iya Ficewa Daga APC
