Ndume Ga El-Rufai: “Alhakin Amaechi Ne Yake Bin Ka”

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya ce wani lokaci yana jin kamar ya yi murna da rikicin da ke faruwa tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Ndume, wanda ya kasance Darakta Janar na yakin neman takarar shugaban kasa na Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa El-Rufai ya kasance cikin tafiyar Amaechi kafin daga bisani ya sauya ra’ayi ya koma goyon bayan Tinubu gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.

A wata hira da aka yi da shi a Arise News ranar Talata, Ndume ya bayyana cewa wannan sauyin da El-Rufai ya yi na iya zama daya daga cikin abubuwan da ke haddasa bacin ransa da kunci a halin yanzu.

A cewar Ndume, “El-Rufai ya kamata ya kasance a gefenmu, amma daga baya sai ya sauya ra’ayi. Kuma ina ganin wannan yana cikin abubuwan da ke bata masa rai ko damunsa.”

Ya kara da cewa: “Ya kasance a gefenmu. A gefen Amaechi. Kafin a tsaida Tinubu, ya yanke shawarar goyon bayansa. Tinubu kuma, kamar yadda ya fada, ya roke shi da kada ya bar tafiyar, ya shigo cikin gwamnati.”

Ndume ya ce tun daga lokacin, dangantakarsa da El-Rufai ba ta kasance yadda take ba domin ya bar tafiyarsu. “El-Rufai ya yi amfani da duk wata dama da ya ke da ita wajen tallafa wa Tinubu. Ya yi aiki sosai. Tinubu ya roke shi da ya shiga gwamnati, amma har yanzu ban gane abin da ya faru tsakaninsu ba. Wannan kuma ba matsalata ba ce.”

Sanatan ya ci gaba da cewa: “Amma wani lokaci, sai in ce, ‘toh, me ka yi mana, yanzu ka dawo kana karbar sakamakon abin da ka aikata da kanka’. Ina rike da mukamin Chief Whip lokacin da El-Rufai ya zo majalisa don tantance shi a matsayin minista, kusan mu ce kawai ya tafi.”

A baya, bayan samun nasarar zabe, Tinubu ya bayyana sunan El-Rufai a cikin jerin sunayen ministocinsa, amma Majalisar Dattawa ta ki amincewa da nadin nasa.

Tun daga nan ne El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), inda ya zama daya daga cikin manyan masu adawa da gwamnatin Tinubu.

More from this stream

Recomended