Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Buba Marwa, ya ce hukumar ta kama tan 761,000 na haramtattun kwayoyi tsakanin watan Janairun 2021 zuwa Maris 2024.
Mista Marwa ya bayyana haka ne a yayin taron Juma’a na musamman a wani bangare na gudanar da bukukuwan ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya ta shekarar 2024 a babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
An kebe ranar 26 ga watan Yuni na kowace shekara domin tunawa da ranar kuma taken ranar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta duniya ta 2024, WDD, ita ce: “Shaida a bayyane take, Mu saka hannu don rigakafi.”
Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce binciken da aka gudanar a shekarar 2018 na amfani da miyagun kwayoyi ya nuna miliyan 15 na ƴan Najeriya ne ke shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda suka ce ya ninka matsakaicin adadi sau uku a duniya.
Mista Marwa, wanda ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba za a amince da shi ba, ya ce manufar shekarar 2024 ta Ranar Magunguna ta Duniya, WDD, ita ce, Ƙoƙarin kiyayewa shi ne Kariya.