NDLEA Ta Kama Ƴar Indiya Da Hodar Iblis A Filin Jirgin Kano

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta cafke wata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu tana ƙoƙarin shigo da hodar iblis cikin tarkacen alewa a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke Jihar Kano.

A cewar hukumar, jami’anta sun samu bayanan sirri kan jigilar kwayoyin ne, wanda ya kai nauyin kilogiram 11, an kuma shigo da su ne daga Bangkok, Thailand, ta ƙetare Vietnam da Doha cikin jirgin Qatar Airways QR1431 a ranar 14 ga Maris, 2025.

Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa Neetu ta ƙara nuna yunkurin masu safarar miyagun kwayoyi na amfani da fararen fata da baƙin haure wajen jigilar kaya haramtattu zuwa Najeriya.

A wani samame daban da aka kai a Kano, jami’an NDLEA sun cafke wani mutum mai suna Michael Ogundele da tukunyar gas din ƙarfe mai girma a Gadar Tamburawa da ke kan titin Zaria-Kano. Da aka fasa kwalbar, an gano ƙwayoyin tramadol 225mg guda 50,000 a cikinta.

Har ila yau, a ranar 19 ga Maris, 2025, an kama Sunday Ogar da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 27 a yankin Gunduwawa, sai kuma wata mata mai suna Khadijah Abdullahi da aka cafke da kwalaben maganin tari mai sinadarin codeine guda 424 a unguwar Lungun Bulala Yalwa a ranar 18 ga Maris.

More from this stream

Recomended