Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani attajirin dan kasuwa mai suna Arokodare Damil Ebenezer, wanda ke da sansanin kasuwanci a Lekki, Lagos, bisa zargin shigo da haramtattun kwayoyi daga Amurka.
A cewar hukumar, an kama Arokodare ne a ranar Litinin yayin da yake jiran karbar sabbin kayansa na miyagun kwayoyi a Bay Lounge, Admiralty Way, Lekki, inda ake zargin yana gudanar da kasuwancin kwayoyi.
Hukumar ta bayyana cewa an samu buhunan tabar wiwi mai nauyin 32.24kg daga hannunsa.
Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama Arokodare ne bayan da aka cafke wasu kaya da aka shigo da su cikin manyan akwatuna guda bakwai a Lagos a ranar 12 ga watan Maris.
Bayan bincike a gidansa da ke Lekki, an kuma samu wasu karin gram 94 na tabar wiwi da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen sarrafa kwayoyi.