Wani abun fashewa da ake kyautata zaton nakiya ce ta fashe yan mitoci kadan daga ofishin sakatariyar jam’iyar APC ta jihar Rivers dake birnin Fatakwal.
Hakan ya haifar da zaman d’ar-d’ar a yankin. Jami’an tsaro da aka jibge a sakatariyar jam’iyar ta APC sun garzaya ya zuwa wurin da nakiyar ta fashe amma wasu yan daba da ake tunanin sun jefar da nakiyar sun tsere a wata mota kirar Toyota Camry wacce ta kai su wajen.
Tun da fari wani abu ya fashe da misalin karfe 11 na safe a wani wuri na daban dake birnin na Fatakwal mai cike da arzikin mai.
Jam’iyar PDP da APC na gudanar da zaben fidda gwanin yan takarar gwamna duk a rana daya a birnin.
Ya yin da PDP ke gudanar da nata taron a filin wasa na Shark dake Fatakwal akwai rudani a jam’iyar APC,bangarori biyu dake biyayya ga Sanata Magnus Abe da kuma bangaren dake biyayya ga ministan sufuri Rotimi Amaechi sun shirya gudanar da zaben a wurare daban-daban.
Magoya bayan Amaechi sun shirya gudanar da nasu zaben a sakatariyar jam’iyar dake jihar.