Najeriya ta buɗe iyakokinta da Jamhuriyar Nijar

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Ya kuma ba da umarnin dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar ta Nijar nan take.

“Shugaba Tinubu ya kuma amince da dage takunkumin kudi da tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Guinea,” in ji wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta zo ne da taken ‘Najeriya ta bude iyakokin kasa da ta sama da jamhuriyar Nijar, tare da dage wasu takunkumin.

More News

An kama mutane biyu  masu garkuwa da mutane a jihar Kogi

Wasu ɓatagari biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne jami'an ƴan sanda da haɗin gwiwar ƴan bijilante suka kama a garin Ibobo-Abocho...

Jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a Akwa Ibom

Wasu ma'aikatan kamfanin haƙar man fetur su 6 da kuma matuƙan jirgi su biyu su mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a...

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naɗa

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...