Najeriya: Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 na N8.83tr

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar da ya kai naira tiriliyan 8.83 ga majalisar dokokin kasar.

An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta sayar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a ko wace rana.

Kuma an tsara kasafin ne bisa hasashen farashin danyen mai kan dala $60 kan ko wace ganga. Kuma kan farashin canji N305 kan dala daya.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2019.

Shugaban ya ce wannan shi ne jawabinsa na karshe na gabatar da kasafin kudi a majalisar dokokin kasa ta takwas.

A jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan shugaban ya ce an samu raguwar hauhawan farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo ma sa sowa da ihu daga bangaren ‘yan adawa a zauren majalisa.

An ji wasu suna cewa “Karya ne,” yayin da Buhari ke bayyana nasarorin gwamnatinsa. Wasu ‘yan majalisar kuma sun ta yi masa tafi domin karfafa masa guiwa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki da yawa duk da ba ta samu kudi da yawa ba.

Sai dai ya ce a kasafin kudin na 2019, akwai triliyan 2.14 da aka ware domin biyan bashi.

Kasafin na badi ya zarce na bara inda shugaban ya ce gwamnatinsa za ta fi mayar da hankali wajen kammala ayyukan hanyoyi da wasu na ci gaba da aka soma.

Za mu ci gaba da kawo maku karin bayani.

More from this stream

Recomended