Najeriya: Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Shugaban PDP

Jam’iyyar PDP reshen jihar Legas, ta yi kira ga jami’an tsaro da hukumomin gwamnati da su sa kokari cikin gaggawa don ganin an sako shugaban jam’iyyar da aka sace, Philip Aivoji.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na jihar Legas, Alhaji Hakeem Amode, ne ya yi wannan kira a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, yana mai cewa: “An sace Aivoji ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Janairu da misalin karfe 6:00 na yamma a kan hanyar Legas zuwa Ibadan yayin da yake dawowa daga taron masu ruwa da tsaki a jihar Oyo wanda Gwamna Seyi Makinde da Gwamna Ademola Adeleke na Osun suka kira.

“Abin takaici ne yadda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kasarmu, kuma gazawar gwamnati na magance wannan matsala abin damuwa ne matuka.”

Sace Aivoji ya nuna matukar bukatar daukar kwararan matakai daga gwamnati da masu ruwa da tsaki don kawar da wannan matsalar.”

More from this stream

Recomended