Tsohon mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya bayyana cewa ya ƙirƙiro labarin cewa beraye sun mamaye Fadar Shugaban Ƙasa a shekarar 2017 ne domin karkatar da hankalin jama’a daga jita-jitar rashin lafiyar Buhari.
Shehu ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafinsa da aka wallafa kwanan nan, mai suna “According to the President: Lessons from a Presidential Spokesperson’s Experience”. A cikin babi na 10 na littafin, wanda aka lakaba “Rats, Spin and All That”, Shehu ya bayyana yadda ya yi amfani da wannan labari a lokacin da shugaban ƙasa ya dawo daga jinya amma bai koma bakin aiki kai tsaye ba.
A cewarsa, bayan wani hadimi na shugaban ƙasa, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa Buhari zai ci gaba da aiki daga gida, ‘yan jarida da dama sun fara neman ƙarin bayani, ciki har da BBC Hausa, inda suka tambayi irin berayen da za su iya cin wayoyin lantarki a Villa.
Garba Shehu ya ce domin kau da hankalin ‘yan jarida daga tambayoyi kan lafiyar Buhari, sai ya danganta lamarin da wani labari da ya faru a shekarun 1980 lokacin da jiragen ruwa suka kawo shinkafa daga ƙasashen Asiya, inda aka ce beraye sun mamaye kaya a tashar jiragen ruwa.
Sai dai ya ce daga baya, Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed, da Mataimakin Shugaban Ƙasa a wancan lokaci, Farfesa Yemi Osinbajo, sun kalubalanci wannan mataki nasa, inda suka bayyana cewa bai dace ba.
Shehu ya dage cewa ya yi amfani da dabarar da gangan, kuma ya gamsu da yadda ta taimaka wajen kawar da hankalin jama’a daga batun lafiyar Buhari a lokacin.
Na Kirkiri Labarin Beraye A Ofishin Shugaban Kasa Ne Don Kare Lafiyar Buhari Daga Cece-kuce—Garba Shehu
