Mutumin da ya jefar da kanwarsa don ‘gudun gori’

[ad_1]

Mai unguwa Mai Fada

Image caption

Mai Unguwa Mai-Fada Ali ne marikinta a yanzu, bayan da aka kai ta majalisarsa da aka tsince ta shekara kusan 16 da ta gabata

Masu unguwanni da dagatai na cikin shugabannin al’umma wadnda a kan garzaya wurinsu da yaran da aka tsinta, mai yiwuwa saboda tunanin da ake da shi cewa su ne suka fi sanin matsalolin al’umma da hanyoyin magance su.

Alhaji Mai-Fada Ali, shi ne mai unguwar Gama B a yankin Brigade da ke birnin Kano, kuma gidansa ya zama tamkar wata cibiya ta kai yaran da aka tsinta, inda daga nan shi kuma sai ya kai su wajen hakimi har a sada su da gidan marayu.

A dalilin irin yawan yaran da ake kai masa akai-akai, har ya kasance yana rikon biyu daga cikinsu a yanzu haka.

Rakiba (ba sunanta na gaskiya ba), mai shekara 18, na daga cikin yara biyun da mai unguwa yake rikonsu, inda ya zame musu uwa da uba da danginsu.

Ya shaida wa BBC cewa, “An kawo ta cigiya majalisata ne a lokacin da ba ta wuce shekara biyu da haihuwa ba, aka ce a Layin Takari aka tsinto ta an ajiye ta tana ta kuka.

Sai na karbe ta ta kwana washegari aka bai wa hukuma ita, amma sai wata mata ta bukaci a bata rikonta. Daga baya ta dawo da ita saboda ta fara fuskantar kalubale daga wajen dangin mijinta.

Image caption

Wasikar da yayan yarinyar ya aike wa mai unguwa a shekarar 2017 yana shaida masa cewa shi ya yar da ita don tserar da ita daga gori

Mai unguwa dai ya nuna min wata takarda, wacce ya ce a shekarar da ta gabata ne wani mutum ya aiko masa, a ciki yana ikirarin cewa shi yayan yayrinyar farko ne, kuma shi ne ya jefar da ita shekaru da dama da suka wuce.

Ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda azabar da dangin mahaifiyarsu ke gana mata bayan mutuwar uwar tasu, sakamakom zargin cewa ba ta hanyar aure ta haife ta ba.

Shi kuma kamar yadda ya ce a wasikar, ya yi kankantar da zai iya kare kanwar tasa daga kalubalen da take fuskanta, shi ya sa ya yanke shawarar ajiye ta a inda ya san za a tsince ta, ya kuma bibiyi inda aka kai ta.

Sai dai wani abun jaje shi ne rashin sake bullowar wannan bawan Allah kamar yadda ya yi alkawarin cewa zai koma ya dauki Rakiba.

“Na jira dawowarsa amma har yau shiru ba amo ba labari shekara daya kenan da kawo wannan wasikar,” a cewar Mai Unguwa.

Image caption

Yarinyar rike da kayan da aka tsince ta da su a jikinta tana ‘yar shekara biyu

A hirar da na yi da Rakiba dai ta shaida min cewa bayan an samu wannan wasika ta fara murnar haduwa da danginta, amma da aka shafe lokaci yayan nata da ya aika wa Mai Unguwa wasikar bai dawo ba har aka shafe tsawon lokaci kamar yadda ya yi ikirari, sai jikinta ya yi sanyi.

“A yanzu dai kam ina fatan idan har ina da rabon ganin jinina to Allah ya sada mu da alkhairi, idan kuma babu rabon ganawa to Allah ya kara min dangana, Baba Mai Unguwa ma ya ishe ni rayuwa, in ji Rakiba.

[ad_2]

More News

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye aikinsa na wani lokaci

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wani lokaci domin tunkarar matsalar lafiya.Mista Ngelale...

Ali Jita ya koma jam’iyar APC daga NNPP

Mataimakin shugaban majalisar dattawa dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi fitaccen mawakin Kannywood, Aliyu Isa Jita daga jam'iyar NNPP ya zuwa jam'iyar APC. Ali Jita...

An yi jana’izar mutumin da ya Æ™irÆ™iri tutar Najeriya

Iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi mutumin da ya ƙirƙiro tutar Najeriya sun yi bikin binne shi bayan da gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin...

‘Za a Æ™ara wa Æ´an bautar Æ™asa na NYSC alawus’

Babban daraktan hukumar yi wa kasa hidima ta kasa (NYSC) Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa ‘yan bautar kasar cewa za a kara...