Mutumin da ya jagoranci fashin garin Offa ya mutu

Michael Adikwu, mutumin da ake zargi da shiryawa tare da aikata fashi da makami kan wasu bankunan kasuwanci dake garin Offa na jihar Kwara, ya mutu.

Kamaldeen Ajibade, kwamishinan shari’a na jihar shine ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da sauran mutane biyar da ake zargi a gaban babbar kotun jihar Kwara.

Adikwu wanda korarren ɗansanda ne ya bayyana cewa ya kashe mutane sama da 20 ya yin fashin da ya jawo asarar rayuka 33 ciki har da wata mace mai ciki da kuma ƴansanda 12.

Akwai dai rahotannin dake cewa jami’an tsaro sun harbe Adikwu ne a gaban sauran mutanen domin tsorata su kan su amince da wata bukata.

Ajibade ya fadawa kotun cewa akwai bukatar a gyara tuhumar da akewa Adikwu sakamakon mutuwar sa.

Inda ya roki kotun da ta dage zaman sauraron shari’ar domin bawa ofishinsa damar sake sabunta tuhumar da ake musu.

Binciken da rundunar ƴansanda ta gudanar ya nuna cewa yan fashin na da alaka da shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki zargin da Saraki ya musalta.

More from this stream

Recomended