
Hukumar dake kula da aikin ƴansanda ta ce mutane 104,289 ke neman a ɗauke su aikin ɗansanda cikin ƙananan jami’an ƴansanda 10000 da za a dauka.
Hukumar ta samu bukatar neman daukar aikin daga mutane 21,878 a ranar 4 ga watan Disamba kwana biyar bayan da aka bude shafin yanar gizo na neman aikin.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya amince a dauki kananan jami’an ƴansanda 10,000 domin kara karfin rundunar.
Ikechukwu Ani,mai magana da yawun rundunar shine ya bayyana haka kwanaki 12 da aka bude shafin yanar gizo na daukar aikin.
Ani ya ce yawan masu neman daukar aikin ya kai mutane 104,289 da karfe 1:30 na daren ranar Talata.
Ya ce za a rufe shafin yanar gizon ranar 11 ga watan Janairu.