Filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe na Abuja
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan batun binciken da jami’ai suka gudanar kan tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar bayan komawarsa kasar daga Dubai.
Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ne ya mayar da wannan martanin a wani sako na Twitter da ya wallafa a shafinsa.
A cikin sanarwar ya soki kalaman tsohon mataimakin shuganban kasar, wanda shi ma ya wallafa a nasa shafin na Twitter, inda ya zargi jami’an shige da fice da bincikarsa tare da tawagarsa da niyyar tozarta shi.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su sani cewa daya daga cikin kudurorin da Atiku tare da tawagarsa suka tattauna a taronsu na Dubai shi ne za su fara cusa wa ‘yan Najeriya tsoro a zukatansu, kuma wannan na daya daga cikin matakan da suka shirya aiwatarwa.”
- Jami’an tsaron Najeriya ‘sun binciki Atiku’
- ‘Ba mu ji dadin bincikar Atiku ba’
Hakkin mallakar hoto
Getty Images
Atikiu Abubakar
Sanarwar ta kuma ce a hukumance, dukkan fasinjoji da suka shigo Najeriya na fuskantar bincike daga jami’an shige da fice, da na kwastam da na kiwon lafiya da kuma jami’an tsaro.
Kuma idan idan jirgin saman da aka yi amfani da shi ba na fasinja ba ne, kamar irin wanda dan takarar jam’iyyar PDPn yayi amfani da shi, to jami’an shige da fice da na kwastam har da sauran jami’an tsaro kan tarbi jirgin su gudanar da bincike a kan jirgin da dukkan wadanda ke cinkinsa.
Sanarwar ta kuma ce ministocin gwamnati ma basu tsira ba daga wannan binciken, illa shugaban kasa:
“Ya kamata a lura cewa ko a bangaren filin jirgin sama da shugaban kasar Najeriya ke amfani da shi, akwai irin wadannan jami’an, wadanda kan duba fasfon shugaban kasa a duk lokacin da ya shiga kasar.
Sanarwar ministan sufurin jiragen saman ta kuma ce, “Binciken da aka gudanar a kan Atiku Abubakar ya zama wajibi, a kan gudanar da shi kan dukkan matafiya da suka shiga Najeriya daga kasashen waje, kuma haka ake yi a sauran kasashen duniya.”
A karshe sanarwar ta yi kira ga yan Najeriya da su “Cigaba da mutunta dokokin kasar”, kuma ta yi kira ga “Manyan mutane da su daina neman daukaka kansu bisa ‘yan kasar da suke son jagoranta”.