Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) ta karyata rahotannin da ke yawo cewa Fulani na shirin kai hare-hare a wasu yankunan kananan hukumomin Barkin Ladi, Mangu, Bokkos da Bassa a Jihar Filato.
Shugaban kungiyar a jihar, Yusuf Ibrahim Babayo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Jos, babban birnin jihar.
A cewar Babayo, “An yada wani labari na bogi da ke zargin cewa mun gudanar da taruka a wurare daban-daban, ciki har da wani masallaci a Mahanga, domin tsara hare-hare yayin watan Ramadan.”
Ya ci gaba da cewa, “Mun yi Allah-wadai da wadannan tuhume-tuhumen karya da aka kirkira. Wadannan zarge-zargen marasa tushe na neman bata mana suna, da yada munanan tunani kanmu, tare da nuna bambanci ga al’ummarmu.”
Babayo ya yi zargin cewa wadannan jita-jita an kirkire su ne domin karkatar da hankalin jami’an tsaro, tare da ba wa wasu damar kai farmaki kan al’ummar Fulani a yankin.
Saboda haka, kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su kare al’ummarta, tana mai nuna damuwa kan tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
“Muna rokon GOC na Runduna ta 3, da Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Folusho Oyinlola, da Kwamishinan ‘yan sanda, Emmanuel Adesina, da su gudanar da cikakken bincike kan wadannan zarge-zargen domin a gano gaskiya,” in ji shi.
Kungiyar ta bayyana cewa tana da yakinin wadannan bayanai na bogi an kirkire su ne domin haifar da rikici da tayar da hankula a jihar.
Miyetti Allah Ta Karyata Zargin Shirin Kai Hari a Wasu Yankunan Filato
