Me ya sa Najeriya ke kan gaba wajen bahaya a fili?

bahaya a fili

Matsalar yin bahaya a filin Allah na ci gaba da zama wata babbar matsalar tsafta a kasashe masu tasowa kamar Najeriya.

A wurare da dama na yankunan karkara har da birane, wasu mutane kan yi bahaya a waje ba tare da la’akari da illar hakan ka iya shafar lafiya al’umma ba.

Wani kiyasi na hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dai ya nuna cewa kasar ce ta daya a Afirka, haka kuma ta biyu a duniya a jerin kasashe masu fama da matsalar yin bahaya a waje.

Latsa alamar laifikar da ke kasa don sauraron rahoton da wakilinmu
A kan wannan dalili ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana dokar ta-baci a bangaren samar da ruwa da tsaftar muhalli a ranar Alhamis.

Da yake magana a wajen taron farfado da samar da ruwan sha da tsaftar muhalli da aka yi ya ce, “A yanzu kasarmu ce ta biyu cikin jerin kasashen da ka fi yin bahaya da fitsari a fili a duniya, inda kashi 25 cikin 100 ke irin wannan halayya.

Mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina ya ambato Shugaba Buhari na cewa: “An samu raguwa a samun ruwan sha na famfo daga kashi 32 cikin 100 a 1990 zuwa kashi bakwai cikin 100 a 2015, haka kuma an samu raguwa a fannin tsaftar muhalli daga kaso 38 cikin 100 zuwa kashi 29 cikin 100 a shekarar 2015.”

Shugaban kasar ya bayyana lamarin yawan bahaya a fili a matsayin babban abin damuwa, ya kuma yi gargadi cewa nan gaba gwamnatin tarayya za ta dinga goyon bayan gwamnatin jihohi ne kawai idan suka nuna jajircewarsu a bangare samar da ruwa da tsaftar muhalli daga nan zuwa shekarar 2025.

“Ba za mu iya kuma ba za mu ci gaba da barin wadannan abubuwa da za a iya hana faruwarsu su ci gaba da rusa mana al’umma ba,” in ji Shugaba Buhari.Shugaba Buhari ya ayyana dokar ta-baci kan tsaftar muhalli

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon É—an majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...