Wani mazaunin yankin ya fadawa Jaridar The Cable cewa sojoji sun tattaru domin zuwa yankin a kokarin da suka yi na dakile harin.
Molai shine kauye ɗaya tilo a bangaren da ba a kaiwa hari ba cikin watanni biyu da suka wuce.
Dalori, Konduga, Dala Shuwa, Dala Karamsu, Mammanti, Zabarmari dukkanin garuruwan sun fuskanci hare haren mayakan kungiyar Boko Haram a yan kwanakin nan.
Ana cigaba da nuna damuwa kan yadda hare haren yan kungiyar Boko Haram ke karuwa a yan kwanakin nan.
A ranar Juma’a mayakan kungiyar sun kai hari garin Gudumbali a karamar hukumar Guzamala inda suka fatattaki sojoji tare da yin awon gaba da motoci masu dauke da bindiga.
Wasu daga cikin sojojin da abin ya shafa yanzu haka suna samun mafaka a wani sansanin soji dake Damasak mai makotaka da garin.
Kwana ɗaya da ya wuce a kalla manoma 12 aka kashe ya yin wani hari da aka kai Zabarmari.
Da yake magana da jaridar The Cable ranar Lahadi wani mazaunin yankin ya ce,”Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe manoma 7a gonakin shinkafa dake Zabarmari a ranar Asabar.
“Mun gano karin wasu gawarwaki biyar a yau, wasu manoman da dama kuma sun bace.”