Matsin rayuwa ya sa wani ɗansandan Najeriya ya halaka kansa

Wani Sufeto Dasu Kassa ya rasu a jihar Adamawa. 

Rahotanni sun bayyana cewa, an tsinci Kassa a gidansa da ke Anguwan Yungur a karamar hukumar Girei da yammacin ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa a lokacin ya dawo ne daga wani asibiti a Yola, babban birnin jihar da yammacin wannan rana. 

A halin yanzu ana ci gaba da binciken al’amuran da suka shafi mutuwarsa.

SaharaReporters ta bayyana cewa matsin tattalin arziki ne ya tilasta masa kashe kansa.

More from this stream

Recomended