Matsalar Sufuri a Babban Birnin Tarayya Abuja

Mutane kan shafe sa’o’i suna jiran mota musammam ma alokutan zuwa aiki da bayan an tashi daga aiki. Wasu daga cikin fasinjojin sunyi korafin yadda sai mutum yana da karfi kafin ya samu shiga mota, haka kuma akan shafe sa’o’i saboda cunkoso kafin mutum ya kai inda ya nufa.

Wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar, ta ji ta bakin wasu ma’aikata da ke fuskantar matsalar sufuri a Abuja. Wadanda suke kira ga gwamnati da ta shiga lamarin domin samun mafuta.

Haka zalika direbobi masu jigila tsakanin Abuja da kauyuka na korafin rashin tsaro, domin wasu lokutan sukan sami ‘yan daba da suke yiwa fasinjoji fashin wayoyinsu a cikin mota.

Akan sami cincirindon mutane a kusan kan kowaccce kwana a babban birinin taryya Abuja, musamman a lokutan da ake tashi daga aiki sakamakon kalubalen sufuri da mazauna yankunan ke fuskanta, lamarin da ke zama abin tausayi musamman ma a lokacin damuna.

More from this stream

Recomended