Rundunar ‘yan sandan Jihar Lagos ta cafke wani matashi mai shekaru 23, Gbolahan Adebayo, bisa zargin dukan budurwarsa har lahira.
Lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Fabrairu, 2025, a unguwar Ijedodo, Isheri-Osun.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Litinin.
A cewarsa, “Wani makwabci ya shaida mana cewa ya ga mutumin yana dukan budurwarsa a dakinsa, ba tare da sanin dalili ba. Bayan ‘yan mintuna, sai wanda ake zargin ya fara kururuwar neman taimako.”
Makwabcin ya ce da ya shiga dakin, ya tarar da budurwar tana kwance ba ta motsi, tare da alamun duka a jikinta.
An garzaya da ita zuwa wani asibiti a Ijegun, inda aka tabbatar da rasuwarta.
Rundunar ‘yan sanda ta ce an kama wanda ake zargi kuma bincike na ci gaba.
Matashi Ya Kashe Budurwarsa Bayan Ya Yi Mata Duka
